1 Corinthians 3

A kan Tsattsaguwa A cikin Ikkilisiya

1ʼYanʼuwa, ban iya yi muku magana kamar masu ruhaniya ba, sai dai kamar masu halin mutuntaka-jarirai cikin bin Kiristi kawai. 2Na ba ku madara ba abinci mai tauri ba, domin ba ku balaga ba a lokacin. Kai, har yanzu ma, ba ku balaga ba. 3Har yanzu kuna rayuwa bisa ga halin mutuntaka. Da yake akwai kishi da faɗace-faɗace a cikinku, ba rayuwa irin ta halin mutuntaka ke nan kuke yi ba? Kuma ba rayuwa irin ta mutane ce kawai kuke yi ba? 4Gama saʼad da wani ya ce, “Ni na Bulus ne,” wani kuma ya ce, “Ni na Afollos ne,” ba rayuwa irin ta mutane ke nan kuke yi ba?

5Shin, wane ne Afollos? Wane ne kuma Bulus? Ai, bayi ne kawai waɗanda ta wurinsu kuka gaskata-kamar yadda Ubangiji ya ba kowannensu aikinsa. 6Ni na shuka iri, Afollos kuma ya yi ban ruwa, amma Allah ne ya sa irin ya yi girma. 7Don haka, da wanda ya yi shuki, da wanda ya yi ban ruwa, ba a bakin kome suke ba, sai dai Allah kaɗai, mai sa abubuwan su yi girma. 8Mutumin da ya yi shuki, da mutumin da ya yi ban ruwa nufinsu ɗaya ne, kuma kowannensu zai sami lada gwargwadon aikinsa. 9Gama mu abokan aiki ne na Allah; ku kuwa gonar ce ta Allah, ginin Allah kuma.

10Ta wurin alherin da Allah ya ba ni, na kafa tushen gini kamar ƙwararren magini, wani kuma dabam yana gini a kai. Amma kowa yǎ lura da yadda yake gini. 11Gama babu wanda zai iya kafa wani tushen gini dabam da wanda aka riga aka kafa, wanda yake Yesu Kiristi. 12In wani ya yi gini a kan tushen ginin nan da zinariya, azurfa, duwatsu masu daraja, itace, ciyawa ko kara, 13aikin zai bayyana kansa, domin za a nuna shi a sarari a Ranar. Wuta ce za ta bayyana aikin, wutar kuwa za ta gwada ingancin aikin kowa. 14In abin da kowane mutum ya gina ya tsaya, zai sami lada. 15In ya ƙone, zai yi hasara, amma zai sami ceto, sai dai kamar wanda ya bi ta tsakiyar wuta ne.

16Ashe, ba ku sani ba cewa ku kanku haikalin Allah ne, Ruhun Allah kuma yana zaune a cikinku? 17Duk wanda ya ɓata haikalin Allah, Allah zai ɓata shi, don haikalin Allah mai tsarki ne, ku ne kuwa haikalin nan.

18Kada ku ruɗi kanku. In waninku yana tsammani cewa yana da hikima, yadda duniya ta ɗauki hikima, to, sai ya mai da kansa “wawa” don yǎ zama mai hikima. 19Gama hikimar duniyan nan, wauta ce a gaban Allah, kamar yadda yake a rubuce cewa: “Yakan kama masu hikima a cikin makircinsu”
Ayu 5.13
;
20kuma a rubuce yake cewa, “Ubangiji ya san dukan tunanin masu hikima banza ne.” 21Saboda haka, kada wani yǎ yi taƙama da mutum! Gama kome naku ne, 22ko Bulus ko Afollos ko Kefas ko duniya ko rai ko mutuwa ko abubuwa na yanzu ko na nan gaba—ai, duka naku ne, 23ku kuwa na Kiristi ne, Kiristi kuma na Allah ne.

Copyright information for HauSRK